Domin Duba Sauran Jawabai Muhimmai daga Alqalamin Ismail Hussaini Adam Alpholtawy Latsa Wannan Butun Butumin đ¤.
‘TSAKANIN UKRAINE DA RUSSIA’
Fayyataccen sharhi daga “Mohiddeen Ahmad”
YaĆin Duniya: Me Ka Sani Game da Ćasashe?
…taĆaitaccen bayani game da YaĆin Duniya –Rikicin Russia da Ukraine da mu’amalarsu da sauran Ćasashe
1.0 Gabatarwa
Duk wani dattijon da bai wuce shekaru 70 ba, to haĆiĆa ba shi labarin abun da ya faru a YaĆin Duniya I da II aka yi, to ballantana kuma matashin da bai wuce 40 ba, ko kuma mu jarirai. Don haka ba mu san yaĆi ba, kuma ba mu san wace illa yake tattare da shi ba. Amma duk wanda ya amsa sunansa “mutum” da ke rayuwa a gabas-maso-arewacin Nigeria, to haĆiĆa ya san “yaĆi” walau kai-tsaye ko ta bayan fage.
An yi YaĆin Duniya I daga shekarar 1914-1918, an yi na II daga 1939-1945; Ćan Adam ya kalli tashin hankalin da bai taÉa gani ba, an kashe miliyoyin mutane, an karya tattalin arziĆin duniya, an wahalar da na wahalarwa, an kashe na kashewa, an kuma durĆusar da na durĆusarwa. HaĆiĆa mun ji labari daga iyaye da kakanni abun babu dadi. Ba ma fatan irin hakan ya sake faruwa.
2.0 Me Ke Faruwa a Yanzu?
2.1 Wacce Ćasa ce Russia?
Russia wata Ćasa ce mai Ćarfin iko a duniya da wani mutum mai suna Vladimir Putin yake mulka a wannan zamanin, karni na 21. Tana da Ćarfin makamai sosai, tattalin arziĆi haÉi da bunĆasa. Wasu abubuwa da za ka iya sani game da ita:
– Ba ta shiri da America da NATO
– Tana Ćawance da China
– Tana da kayan yaĆi Ćwarai da gaske
– Ta ninka Ukraine sau sama da 10 a kayan yaĆi
– Tana da yawan mutanen da suka kai Miliyan 144
2.2 Ina ne Ukraine?
Ukraine wata Ćasa ce da ke gabashin Turai kuma tana makwabtaka da Russia. Da suna zaune cikin lumana kafin Ćudirin sabon shugaban Ćasarsu ya tayar da hatsaniya. Matashin shugaban mai suna Volodymyr Zelensky ya nuna aniyarshi ta shiga Ćungiyar haÉakayyar Ćasashe mai suna NATO. MaĆwabciyarta Russia ta ce a’a. Ga wasu abubuwa da za ka iya sani game da Ukraine:
– Suna da yawan mutanen da ya kai Miliyan 44
– Ukraine tana maĆwabtaka da Russia
– Tana yunĆurin shiga NATO
– Tana tunanin America da NATO sune Ćawayenta
2.3 Mene ne NATO, G7, UN, EU?
– NATO (North Atlantic Treaty Organization) gamayyar Ćasashe ce da aka samar bayan YaĆin Duniya II. Akwai Ćasashe 30 a wannan gamayyar, inda suke yunĆurin bayar da kariyar tsaro ga duk wata memba Éinsu da aka taba. Cikin waÉannan Ćasashe akwai US, UK, Canada, France, Germany, Italy, Portugal, Turkey da sauransu.
– G7 (Group of Seven) wannan ma zauren wasu Ćasashe ne guda 7 da suka haÉa kai don samun wani tagomashi da tallafin juna a Éangaren siyasa da tattalin arziĆi. WaÉannan Ćasashen sune: US, UK, Italy, Germany, Japan, Canada da France.
– UN (United Nations) majalisar Éinkin duniya da aka samar bayan YaĆin Duniya II, inda ta haÉa Ćasashe 193 a cikin 195 da suke duniya.
– EU (European Union) haÉakayyar Ćasashen Turai da ta Ćunshi Ćasashe 27.
– CSTO (Collective Security Treaty Organization) haÉakayyar wasu Ćasashen Soviet Union da suka haÉa da Russia, Uzbekistan, Kazakhstan, Tajikistan, Azerbaijan, Armenia da Georgia da sauransu.
2.4 Mece ce AlaĆar America a Cikinsu?
– America ba ta shiri da Russia
– Russia ba ta shiri da NATO da G7
– Russia tana Ćawance da China da CSTO
– China ba ta NATO da G7; a zahiri ba ta Ćawance da US, NATO ko G7
3.0 Mene ne Silar FaÉan Ukraine da Russia?
Ukraine ta nuna Ćudirinta na son shiga NATO amma sai Russia take son katse mata hanzari. Shugaban Russia Putin ya ce ba zai yiwu ba, don ba zai yarda a masa zagon Ćasa ba. Dalilinsa a nan shi ne, idan ya bari Ukraine ta shiga NATO, kenan an kawo masa maĆiyi har gida tunda ba ya shiri da NATO. Zai fi kyau maĆiyinka ya kasance nesa da kai, don suna maĆwabtaka da Ukraine, kenan duk abun da NATO ta ga dama za ta iya yi a Ukraine din don yi wa Russia zagon Ćasa. Putin ya ce ya gano wannan logar, don haka sai ya Ćudiri aniyar shafe Ukraine a doron Ćasa kafin ta yunĆura.
Ukraine ba ta kai Russia Ćarfin soji ba, ko kusa. Ita kawai ta dogara da NATO da kuma America. Amma NATO ta yi shiru, US kuma tana kallon abun da ke faruwa tana alhini.
4.0 Wane Sakamako Duniya Take Jira?
Duniya tana tunanin YaĆin Duniya III zai iya kaurewa, saboda da zaran NATO da US sun yunĆuro wajen mayar martini ga Russia kan cin zalin da take yi, to haĆiĆa ita ma China da ta kasance Ćawar Russia za ta Ćaddamar da yaĆi a kan NATO da Ćawayenta. Su ma Ćananan Ćwari da ke CSTO za su kai wa Russia agaji a matsayin kara. Wannan kuma shi ake tsoro, domin shi ne zai kasance YaĆin Duniya III a wannan Ćarnin idan ba a yi sulhu ba.
Ba ma fata ko kaÉan, amma idan hakan ta tabbata, to:
– Nahiyar Europe za ta hargitse
– Nahiyar Asia za ta hargitse
– Tattalin arziĆin duniya zai durkushe
– Africa za ta shiga halin ĆaĆa-ni-ĆaĆa
5.0 Rufewa: YaĆi Ćan Zamba Ne!
YaĆi Ćan Zamba ne! America ba za ta shiga kowane faÉa ba matuĆar ba ta yi abun da ake Ćira “analysis” ba. Sai ta caje komai ta tabbatar tana da “interest” kafin ta faÉa.
Zan maimaita, babban fatanmu a nan shi ne sulhu.
Allah Ya tsare mu, amin.
–Mohiddeen Ahmad
24th February, 2022